ilimi
Canjin Zamani: Kano na buƙatar ƙwararru a fannin kimiyya da fasaha
Hukumar kula da makarantun kimiyya da fasaha ta jihar Kano ta ce akwai bukatar iyaye su rika barin “yaya” mata su sami kwarewa a fannin kimiyya da fasaha kamar kowa.
Shugaban hukumar kula da makarantun Alhaji Ahmed Tijjani Abdullahi ya bayyana hakan ga tashar Freedom Radio.
Ya kara da cewa a yanzu haka akwai yara masu yawa dake karatun kimiyya da fasaha a jihar Kano da a dadin ya kusan zarce na maza.
Ya cigaba dacewa “wannan abu na taimakawa matuka musamman a asibitoci mu duba da cewa a yanzu mata ne ke duba yan uwan su mata”
Inda ya kara da cewa ” jihar Kano nada ga cikin jihohi dake da yawaitar makarantu kimiyya a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login