Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hisba ta yi bikin fasa kwalaben giya a Kano

Published

on

Hukumar Hisba a jihar Kano ta yi bikin fasa tarin kwalaben giya da kuɗin su ya kai sama da Naira miliyan 100.

Hukumar ta kama tarin giyar ne a wuraren daban-daban a yunƙurin da aka yi na shigowa da su jihar Kano.

Babban Kwamandan hukumar Shiekh Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya jagoranci fasa kwalaben giyar a ranar Laraba a yankin Kalebawa da ke da nisan kilomita 12 daga shalkwatar ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

Ya ce, an ware ranar ne domin fasa tarin kwalaben giyar a ƙoƙarin hukumar na yin umarni da kyakykyawan aiki da yin hani da mummuna a jihar Kano.

Bikin fasa kwalaben giyar ya samu halartar jami’an tsaro da kuma ma’aikatan gwamnatin jihar.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!