Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake mayar da martani ga roko da Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya yi na tsawaita wa’adin dakaru na musamman a yakin da ake yi da ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da kuma fadada rundunar Operation Safe Heaven a Kudancin Kaduna da Birnin-Gwari da kuma sauran yankunan da ke fama da rikici a jihar a ziyarar da ya kai wa gwamnan ranar Jumma’a.

Da yake mayar da martani ga roko na gwamnan, CDS Musa ya ce, “Duk abin da ke faruwa a yanzu lokaci ne kawai, kuma na san da yadda muke tafiyar da lamarin, nan ba da jimawa ba wannan zai kare”.

“Dukkanmu mun taso ne da sanin yadda Kaduna ta kasance cikin zaman lafiya, kuma yanzu lokacin da muke ciki, na yi imanin cewa lokaci ne kawai, kuma za mu tsallake, kuma ina tabbatar muku da cewa rundunar soji za ta ci gaba da ba ku dukkan abin da ya dace.

Wanda ya ce, yana da matukar muhimmanci ‘yan Najeriya su rungumi kalubalan da ake fuskanta a kasar, inda ta kara da cewa kalubalen rashin tsaro ba na Kaduna ba ne ko sojoji ko ‘yan sanda kadai ba domin kowa na da rawar da zai taka.

Gwamna Sani, ya tabbatarwa da hafsan hafsoshin tsaron kasar kan kudirin gwamnatinsa na ganin an samar da kyakykyawar alaka da hadin gwiwa da hukumomin tsaro da kuma kokarin hadin gwiwa tsakanin jihohi wajen yaki da ta’addanci da ‘yan fashi a jihar Kaduna.

Kamar sauran jihohin shiyyar Arewa-maso-Yamma, jihar Kaduna ta gaji da tabarbarewar tsaro daga ‘yan ta’adda, ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane da barayin shanu.

Sakamakon haka, an yi hasarar rayuka da dama, abubuwan rayuwa sun lalace sannan dubban mutane makiya sun raba su da gidajensu.