Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Champions League: Benfica ta chasa Barcelona da ci 3-0

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Benfica daga kasar Portugal, ta yi nasarar doke Barcelona da ci 3-0 a gasar cin kofin zakarun turai Champions League a ranar Laraba 29 ga Satumbar 2021.

Dan wasan Benfica Darwin Nunez ne ya fara zura kwallon farko a minti na 3 da wasan.

Sai dai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci dan wasa Rafa Silva ya zura kwallo ta biyu a minti na 69 bayan samun tai mako daga hannun dan wasa Joao Mario.

Dab da za’a kammala wasanne aminti na 79 dan wasa Darwin Nunez ya zura kwallo ta 3 kuma ta biyu gareshi a bugun daga kai sai mai tsaran gida, bayan da dan wasan Barcelona Sergino Dest ya taba kwallo a da’ira ta 18.

Nasarar da Benfica ta yi ya bata damar komawa mataki 2 da maki hudu a rukunin E.

Yayin da ita kuma Barcelona take matakin karshe a rukunin da maki 0 a wasanni biyu data buga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!