Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Chelsea na zawarcin dan wasan Najeriya da Napoli, Victor Osimhen

Published

on

Zakarun gasar Champion League a kakar wasanni ta 2020/2021 Chelsea na zawarcin dan wasan gaba na Super Eagles da Napoli Victor Osimhen.

Osimhen dai ya zura kwallaye 6 da kuma taimakawa aka zura kwallo 1 a wasanni 6 da ya buga a kungiyar tasa ta Napoli akakar wasanni da muke ciki ta 2021/2022.

A baya-bayannan dai kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta yi yunkurin siyan dan wasan mai shekaru 22.

Sai dai rahotanni sun bayyana tuni kungiyar Chelsea, Real Madrid, da Paris Saint-Germain ke ci gaba da zawarcinsa.

Dan wasan dai ya taka rawar gani a wasan da  Napoli ta yi  2-2 da Leicester City a gasar  Europa League ta bana.

Osimhen dai kwantaraginsa da Napoli zai kare a shekarar 2025.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!