Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Champions League: Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 136 a gasar

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dake kasar Ingila, Cristiano Ronaldo ya ci kwallo ta136 a gasar zakarun nahiyar turai ta Champions League a wasan da kungiyar kwallon kafa ta Young Boys dake kasar Sweazland ta yi nasara kan United da ci 2 da 1.

An buga wasan dai a yau 14 ga watan Satumbar shekarar 2021 a filin wasa na kungiyar ta Young Boys.

Hakan ya sa dan wasa yake kan gaba da tazarar kwallaye 35 tsakaninsa da ‘yan wasan da suka kai shekara 30 ko fiye da haka da suka ci kwallo a tarihin gasar.

Ronaldo ne ya fara zura kwallo a minti na 13 da fara wasan, inda Young Boys ta farke ta hannun dan wasan ta, Nicolas Moumi Ngamaleu.

Daf da za a tashi Young Boys ta kara kwallon ta biyu ta hannun Jordan Siebatcheu da hakan ya sa ta hada maki uku a karawar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!