Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kalubale ya hana ‘yan wasan Najeriya buga wasanni 100-Enyeama

Published

on

Tsohon mai tsaran gida na Super Eagles Vincent Enyeama, ya alakanta rashin samun ‘yan wasannin kasar nan da gaza buga wasannin 100 ko sama da haka da matsalolin da ake fuskanta a tawagar ta  Super Eagles. 

Enyeama, yace  rashin samun hadin kai da kuma fahimtar juna tsakanin ‘yan wasa da kuma jami’an kungiyoyi ne silar hakan.

A karshen watan Satumba za’a gudanar da zabe a hukumomin wasanni na Najeriya-Sunday Dare

A baya dai ‘yan wasa biyu  ne a tawagar Super Eagles suka iya buga wasanni 100 a kungiyar da suka hada da shi kansa  Enyeama da kuma Joseph Yobo.

‘Yan wasa biyun sun sami damar  lashe gasar kofin nahiyar Afrika a shekarar

2013 da kasar Afrika ta kudu takarbi bakuncin gasar wanda Najeriya tayi galaba kan kasar Burkina Faso daci daya da nema, a wasan karshe.

Da ya ke ganawa da jaridar ESPN, tsohon mai tsaran gida na  Enyimba yace indai ‘yan wasa irinsu  Austin Okocha, Peter Rufai, Nwankwo Kanu da Mikel Obi da wasu ‘yan wasan basu samu damar haka ba lamarain ya zama  abun dubawa.

“Buga wasanni 100 ba wani abu bane, nayi takaici ace ‘yan wasa biyu ne kawai a Super Eagles suka iya buga wadannan wasannin”

“Akalla muna da ‘yan wasa sama da 10 zuwa  15 a yanzu, amma babu wanda ya kai ga buga wasa 100 sabi da rashin tsayayyun masu horarwarwa a kungiyar” a cewar Enyeama

Ya kuma ce ‘yan wasa irinsu Jay Jay (Okocha), Peter Rufai, Mikel da  Kanu sun cancanci ace sun buga wasanni 100, a Super Eagles.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!