Connect with us

Labaran Wasanni

Champions league: Real Madrid ta yi rashin nasara har gida a hannun FC Sheriff

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi rashin nasara har gida a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafar Turai ta Champions League.

Madrid ta yi rashin nasarar ne a hannun kungiyar FC Sheriff da ci 2-1.

Dan wasan kungiyar ta FC Sheriff D.Yakhshibaev ne ya fara zura kwallo a mintuna na 25 da fara wasa.

Kafin daga bisani Dan wasan gaban Real Madrid Karim Benzima ya farke kwallon a bugun dagakai sai me tsaron raga a mintuna na 65.

Dab da tashi daga wasan Dan wasan FC Sheriff ya Kara kwallo a ragar Madrid a mintuna na 89 da wasa.

Yanzu haka dai kungiyar FC Sheriff ce ta 1 a rukun da take na D da maki 6 inda Real Madrid ke biye mata a matsayin ta 2 da maki 3 sai Inter Milan a matsayin ta 3 da maki 1 ita kuwa Shakhtar Donetsk ce a matsayin ta 4 itama da maki 1

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!