Labaran Wasanni
Chelsea ta dauki dan wasa Werner
Kungiyar Kwallon kafa ta Chelsea ta dauki dan wasan gaba mai zura Kwallo na kungiyar Kwallon kafa ta RB Leipzig ,dan kasar Jamus (Germany ) Timo Wener.Mai shekaru 24 , Werner ya sanya hannu a kan kwantiragin shekaru hudu akan kudi fam miliyan 47 kwatankwacin Euro miliyan 53.
Daraktan Kungiyar Marina Garanovskaia, ta tabbatar da hakan inda ta ce, munyi murna kwarai da Werner ya zabi kungiyar Chelsea, kasancewar matashin dan wasa ne haziki da kungiyoyi da dama ke farautar sa , wannan abin alfahari ne , muna masa fatan alheri kafin ya zo nan da watan Yuli.
Shima dan wasan Werner , ya bayyana cewa” yana jiran lokacin da zai fara wasa da abokanan Kwallon sa , da ‘yan kallo da sabon mai horar wa ,ina fatan tare zamu kafa sabbin tarihi a kungiyar nan gaba “.
Dan wasan ya kasance na biyu da kungiyar ta dauka, bayan dan wasan kungiyar Ajax Hakim Ziyech ,kana kungiyar ta Stamford Bridge na zawarcin dan wasan Leverkusen ,Kai Harvetz da na Leicester City Ben Chilwell.
You must be logged in to post a comment Login