Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Katsina United ta musanta rashin biyan ‘yan wasa albashi

Published

on

Mahukuntan Kungiyar Kwallon kafa ta Katsina United, sun musanta labarin da ya karade kafofin sada zumunta cewar ‘yan wasan Kungiyar na bin bashi na watanni bakwai.

Sakataren kungiyar Alhaji Sani Tinau, ne ya bayyana haka a hirar da yayi da sashen yada labarai na kungiyar.

Alhaji Sani Tinau, ya ce tabbas ‘yan wasan na bin kungiyar bashin albashi na wata hudu, ba wai na wata bakwai ba kamar yadda ake rade-radi.

Ya ce a yanzu haka shirye -shirye sunyi nisa na biyan ‘yan wasan hakkin su na baya, wanda halin da aka shiga a kasa na Annobar Corona ne ya janyo hakan.

Sakataren ya kuma bukaci ‘yan wasan, da su kara hakuri kasancewar ana shirin biyan su hakkokin nasu, tare da basu shawarar janye niyyar su ta yin Zanga -zanga a fadar gwamnatin jihar, don ganin bukatar su ta biya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!