Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Chris Ngige : Mun biya alawus na ma’aikatan lafiya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce, ta kashe Naira biliyan goma sha biyar da miliyan dari takwas wajen biyan alawus din ma’aikatan lafiya a asibitocin koyarwa da kuma cibiyoyin lafiya na tarayya da ke fadin kasar nan.

Ministan kwadago da samar da aikin yi, Sanata Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin zantawa da shugabannin kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki jiya a Abuja.

Ya ce, ya zuwa yanzu gwamnati ta biya ma’aikatan bangaren lafiya sama da naira biliyan goma sha biyar a matsayin alawus dinsu na aiki da su ka yi na yaki da cutar covid-19.

Sanata Chris Ngige ya kara da cewa yanzu haka ma’aikatan da ke aiki an biya su alawus din su na watannin Afrilu da Mayu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!