Kiwon Lafiya
Cibiyar AFRI CIRD ta bukaci mahukunta da su dakile ayyukan sayen kuri’u yayin zabe
Cibiyar tattara bayanai a kasashen Afrika da gabatar da rahoto AFRI CIRD ta bukaci mahukunta su tashi tsaye wajen magance dabi’ar sayen kuri’u da wasu daga cikin wakilan jam’iyyu ke yi yayin da ake gudanar da zabe.
Shugaban cibiyar kwamared Muhammad Bello ne ya yi wannan kira ta cikin shirin ‘’Mu leka Mu Gano’’ na musamman na nan Freedom Radio wanda ya maida hankali kan siyen kuri’u da kuma abinda hakan ka iya haifarwa ga siyasar kasar nan.
kwamared Muhammad Bello ya kumma bayyana cewa, sayen kuri’un matsala ce babba da idan ba’a mayar da hankali wajen magance ta ba zata haifar da gagarumar matsala ga cigaban dimukuradiyyar Najeriya.
Haka kuma ya kara da cewa yanzu haka masu sayen kuri’ar na amfani da dabaru wajen karbar katinan zaben mutane tare da basu kudaden da basu taka kara sun karya ba wanda hakan ke sanya su sayar da ‘yancin su.
Shugaban Cibiyar ta tattara bayanai a kasashen Afrika ya kuma shawarci al’umma da su guji yadda da masu basu kudi ko wani abu don sayar da kuri’ar su kasancewar hakan ya saba da dokar hukumar zabe ta kasa.