Labarai
Cibiyar Kwararru kan Hulɗa da Jama’a Reshen Kano ta naɗa Sabbin Shugabanni
Cibiyar kwararru kan hulɗa da jama’a ta Nigerian Institute of Public Relations NIPR reshen Kano ta gudanar da zaɓen sabbin shugabanni domin ci gaba da jan ragamar cibiyar
Cibiyar ta sake ƙaddamar da sabbin shugabannin ne a jiya yayin taron shekara shekara da take gudanar wa damun ƙara tattaunawa kan yadda za’a ƙara inganta harkar hulɗa da jama’a a ma’aikatu da sauran gurare
Alhaji Habibu Bello Dankadai da ya wakilci Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ja kunnan sababbun shugabannin da aka zaba da su fito da hanyoyi na musamman da za su Kara inganta aikin Jarida
Da yake Jawabi sabon shugaban cibiyar ta hurda da jama’a reshen jihar Kano Aliyu Yusuf cewa ya yi, za su hada kan jami’an gwamnati dake ma’aikatu da manyan makarantu da Kuma na kafafen yada labarai wajen zuwa ayi tafiya a tare ta yarda za a Ƙara ciyar da aikin yada labarai gaba
A nasa jawabin gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da kwamishinan yada Labarai Baba Halilu Dantiye ya wakilta cewa ya yi, gwamnati za ta ci gaba da taimakawa cibiyar ta NIPR wajen inganta harkokin yada labarai
Farfesa Abdallah Uba Adamu Malami a sashin koyar da aikin Jarida na Jami’ar Bayero dake Kano ya gabatar da takarda mai taken Kirkirarriyar Fasahar Yada Labarai a fannin hurda da Jama’a Alfahunta da Kuma Kalubalanta
An zabi Aliyu Yusuf a matsayin shugaba sai Isma’ila Ammai Maizare a matsayin mataimaki yayin da Abdullahi D. Abdullahi ya zama ma’aji sai Usman Gwadabe da ya kasance Sakatare da
Muhammad Dahiru Idris a matsayin mataimakin Sakatare ita kuwa Samira Sulaiman an zabe ta a matsayin Jami’ar hurda da jama’a ne sai Abdullahi Abba Hassan da ya kasan ce sakataren kudi da Ado Sa’idu Warawa a matsayin mai binciken kudi
You must be logged in to post a comment Login