Labarai
Cibiyar NCTC da Burtaniya sun karfafa hadin kai don yaki da ta’addanci

Cibiyar yaki da ta’addanci ta Najeriya NCTC karkashin jagorancin ofishin mai baiwa Shugaban Kasa shawara kan tsaro tare da hadin gwiwar kasar Burtaniya sun kara karfafa hadin kai domin kara inganta Shirin kawo Karshen rikice rikice da yaki da ta’addanci a kasar nan
Shugaban cibiyar ta NCTC na kasa Manjo Janar Adamu Laka, ne ya bayyana hakan yayin bude kwas din na musamman ga shugabannin tsaro, na Gold da Silver Commanders tare da nazarin bayanan sirri, a taron da ya gudana a jiya litinin a Abuja
Manjo Janar Laka wanda Birgediya Janar Eromisele lawani ya wakilta ya ce horon wani muhimmin mataki ne na karfafa shirin kasa wajan fuskantar manyan hare hare da kuma rikice rikice cikin gida.
A nasa jawabin mai Kula da yaki da ta’addanci na Burtaniya a yankin Afirka, Lan Tyler ya ce shirin horon wata dama ce ta musamman da ke hada hukumomi Daban -Daban domin Gina sabbin shugabanin tsaro a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login