ilimi
CIBN: Yadda aza harsashin ginin dakin taro ya kasance a kwalejin fasaha ta Kano
Cibiyar kwararrun ma’aikatan banki ta kasa ta kaddamar da harsashin ginin dakin taro a sashen koyar da aikin banki a kwalejin fasaha ta Kano polytechnic.
Cibiyar ta gudanar da bincike tare da tantance kwalejojin fasaha da ke shiyyar Arewa maso yamma kafin ta kai ga ta zabo kwalejin ta Kano
Shugaban kungiyar reshen jihar kano Malam Aliyu Wada Nasir ya ce, samar da dakin taron zai yi tasiri wajen inganta ilimi, kasancewar gwamnati kadai ba zata iya wadatarwa ba.
“Ya kuma ce dakin zai dauki kimanin mutum sama da 160 tare da sanya kayan aiki na zamani ta yadda dalibai zasu samu damar koyan karatu a saukake.
Da yake aza harsashin ginin mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga sauran cibiyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi wajen tallafawa gwamnati domin farfado da harkar ilimi a kasar nan.
“Mun sani jihar Kano na da dumbin matasa da dalibai, don haka ba za a samu bunkasar harkar ilimi ba har sai kungiyoyi da daidaikun jama’a sun tallafawa bangaren”.
Shi kuwa shugaban kwalejin Dakta Kabiru Bello Dungurawa ya tabbatar da cewa za su yi amfani da dakin ta hanyar da ta dace tare alkinta shi don amfanin gaba.
You must be logged in to post a comment Login