Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Cikin makwanni 2: Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 90

Published

on

Shalkwatar tsaro ta ƙasa, ta ce cikin makwanni biyu dakarun Operation Haɗin Kai sun samu nasarar hallaka sama da ƴan Boko Haram da kuma ƴan kungiyar ISWAP 90 da ke Arewa masu Yammacin ƙasar  nan.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar nan birgediya janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a Abuja, lokacin da ya ke gabatar da rahoto kan ayyukan da sojojin suka gudanar daga ranar 11 ga watan Nuwamba zuwa Alhamis 25 ga watan.

Bernard Onyeuko ya kuma ce, an kawar da wasu ƴan ta’adda da ba a kai ga tantance yawan su, a ranar 12 ga watan Nuwamba a yankin Baga kusa da tafkin Chadi.

A cewar sa, a ranar 13 ga watan Nuwamba sojojin sun daƙile harin da ƴan ta’adda suka kai wa sojoji a Askira-Uba da ke Borno, tare da kashe ƴan ta’addar sama da 50.

Cikin rahoton dai, Onyeuko ya ce sojojin sun samu nasarar kama gawurtaccen dan bindigar nan Haladu Saleh wanda take nema ruwa a jallo tun a shekarar 2018.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!