Labaran Kano
Cin amanar al’umma ne ficewar Gwamna Abba daga jam’iyyar mu – NNPP

Jam’iyyar NNPP ta soki matakin da gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta masu kaɗa ƙuri’ar da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen 2023.
Ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson ya fitar, jam’iyyar ta ce matakin da Gwamna Yusuf ya ɗauka tamkar cin amanar al’ummar jihar Kano ne, wanɗanda a cewarta, sun kaɗa masa ƙuri’a ne sakamakon daɗewar da ya yi yana tare da tafiyar siyasar Kwankwasiyya.
Jam’iyyar NNPP ta buƙaci magoya bayanta a Kano da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka, su kuma yi taka-tsan-tsan kan duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma a siyasance ko kuma ta da zaune tsaye.
You must be logged in to post a comment Login