Labarai
Cin zarafin Al-Qur’ani: Gwamnatin Zamfara ta nemi ‘yan jihar su yi Azumin kwanaki 3
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle yayi kira ga musulman jihar da su gudanar da azumin kwanaki 3 da kuma yin addu’o’I don Allah ya hukunta wanda suka sanya wa Alqur’ani Najasa tun a duniya.
Bello Matawalle ya bayyana hakan ne a birnin Gusau ta bakin kakakin yada labaran sa Malam Yusuf Idris.
Rahotanni sun bayyana cewar, tun a shekara ta 2016 ne ake yawan samun wasu na cin zarafin Alqur’ani mussaman a babban birnin jihar ta Gusau.
Haka zalika a kwanan baya ne gwamnatin Zamfara ta sa ayi bincike akan batun sanya Qur’ani a najasa, tayi alkawarin bayar da naira miliyan 2 ga duk wanda ya kawo bayanai
Gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da wani bincike akan sha’anin da ke tattare da al’amarin tsintar wasu fallayen Qur’ani a najasa a makarantar Firamare a ranar Juma’a.
Rubutattu masu alaka:
Tubabbun masu garkuwa sun saki mutane 372 a Zamfara
Ankashe mutane Talatin da biyar a Zamfara
An gano shafukan littafin mai tsarki ne a makarantar Firamare na Shattima, Gusau, wanda yayi sanadiyar rufe makarantar har sai baba-ya-gani da kuma dakatar da malaman makarantar bisa ga umurnin gwamnan jihar, Alhaji Bello Matawalle.
Gwamnan wanda a yanzu haka ya halarci taron zuba jari na Afrika a kasar Amurka, ya umurci hukumar makarantar Firamare da ya kafa kwamitin bincike akan lamarin.
A wani jawabi daga babban sakataren gwamnati Alhaji Bala Maru, a Gusau a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumba, gwamnatin ta sanar da kafa kwamitin mutum 23, karkashin jagorancin Farfes