Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

civil Defense: zata fitar da jadawali na auna yanayin ayyukan kwakwalwarsu

Published

on

Kwamandan rundunar tsaro ta Civil defense Albdullahi Gana ya umarci sashin kula da dabi’u da binciken kwakwaf kan halayyar dan Adam na hukumar ya fitar da jadawalin daukar bayanan sirri na jami’an hukumar wadda ya hada da auna yanayin ayyukan kwakwalwar su.

Matakin ya biyo bayan zargin aika aika akan wani jami’in Rundunar da ake tuhuma da bi ta kan dandazon mutane da mota a garin Gombe a ranar lahadin datata gabata.

Lamarin dai ya faru ne a dai-dai lokacin da wasu matasa dake atisayen motsa jiki a wani bangare na bukukuwan Ester da akayi a makon jiya.

Sai dai a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar Emmanuel Okeh ya fitar a can Abuja ta ruwaito babban kwamandan rundunar ta tsaron ta civil defence ABDULLAHI Gana tilas rundunar ta dauki matakan tantance yanayin kwakwalwar jami’anta.

Yace hakan zai karawa rundunar masaniya dangane da dabi’u da yanayin da suke ciki a lokacin da suke gudanar da ayyukan su.

Sanarwar tace baya ga gwaje gwajen sanain yanayin aikin kwakwalwa, rundunar tsaron ta civil zata fara shirin bada horo ga jami’an nata a dukkanin matakai.

Haka zalika, sanatwar ta baiwa alhinin babban kwamandan rundunar dangane da wancan aika-aika da jami’inta ya yi a Gombe na tuka mota ta kan dandazo mutane lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 9 tare da jikkata wasu da dama.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!