Labarai
Ciwon kunne ya janyo tsaiko a shari’ar Ɗan saruaniya
Kotun majistret mai lamba 58 ƙarkashin mai Shari’a Aminu Gabari ta yi umarnin a tsare injiniya Mu’azu Magaji Ɗan Saruaniya a asibitin Ƴan sanda.
Tun da fari dai an gurfanar da Ɗan saruaniya ne bisa zargin ɓata suna inda aka yi zargin ya saki baki a kan gwamnan Ƙano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
A zaman kotun na ranar Juma’a lauyan Ɗan Sarauniya ya yi suka a kan buƙatur masu gabatar da ƙara waɗanda suka roƙi a karantowa Ɗan Sarauniyar tuhumar da ake yi masa sakamakon baya ji sosai biyo bayan haɗari da yayi.
Yayin da yake ƙwarya-ƙwaryar hukunci mai shari’a Aminu Gabari ya ayyana cewar tabbas wanda yake da matsalar kunne ba za a karanta masa tuhuma ba tunda ba zai iya jin abin da aka karanta ba.
Sai dai kotun ta yi umarni a tsare shi a asibitin ƴan sanda zuwa ranar Litinin wanda ake sa ran ko kunnen na sa zai warke kamar yanda wakilin Freedom Radio Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito.
You must be logged in to post a comment Login