Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gudun wuce sa’a ya haddasa mummunan haɗari a Kano

Published

on

Ana fargabar rasa ran wani direban mota sakamakon gudun wuce Sa’a da yake yi a safiyar ranar Asabar.

Haɗarin ya faru ne a titin Goron Dutse sakamakon taho mu gama da motoci biyu suka yi.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa guda daga cikin motar ita ce ta ke gudun wuce Sa’a wanda hakan ya sa ta je ta bige ɗaya motar da ke gabanta.

Sai dai tuni jami’an ƴan sanda da ke sintiri a yankin suka kai ɗauki tare da gaggawar kwashe waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake duban tsaftar muhalli a yau Asabar, wanda hakan ya tilastawa tawagar tsaftar muhalli ta kai ɗaukin gaggawa wajen ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!