Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Clair Todibo zai koma Barcelona

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Schalke 04, dake kasar Jamus wanda ya zo aro daga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Jean  Clair Todibo, zai koma kungiyar sa ta Barcelona , a karshen gasar kakar wasanni ta bana.

Hakan ya biyo bayan kasa cimma matsaya tsakanin kungiyoyin biyu na Barcelona da Schalke 04, akan daukar dan wasan na din-din  a kungiyar ta Schalke 04, akan kudi Euro miliyan 25, kamar yadda shugaban wasanni na kungiyar Schalke 04, Jochen Schneider ya sanarwa da manema labarai.

Dan wasa Todibo, mai wasa a baya dan kasar Faransa, ya je kungiyar ta Schalke a watan Janairu bana, a matsayin dan wasan aro, wanda kawo yanzu haka kungiyar tayi wasanni goma sha daya ba tare da samun nasara ba, wanda hakan yake babban kalubale ga kungiyar a kokarin data ken a kare matsayinta a gasar ta Bundesliga.

Labarai masu alaka.

Muller ya saka hannu a sabon kwantiragi da Bayern Munich

Yadda Messi ya lashe Ballon d’Or karo na shida

Schneider, ya kara dacewa maganar Todibo, ta wuce kasancewar lokacin da aka diba na cimma matsaya ya wuce don haka ba maganar siyan dan wasan a yanzu haka da kungiyar ke fatan yi a baya.

Clair Todibo,mai shekaru ashirin, ya buga wasanni hudu daya shigo a matsayin canji, a Bundesliga tun bayan dawowar sa gasar daga kungiyar Barcelona , in da ya buga mintuna 363.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!