Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Yadda Messi ya lashe Ballon d’Or karo na shida

Published

on

A ranar 2 ga watan Disambar shekarar 2019 ne hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta  bayyana sunan Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Lionel Messi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya wato Ballon D’or na kakar wasanni ta shekarar 2018/2019.

Messi dan kasar Argentina ya doke babban abokin hamayyar sa Cristiano Ronaldo da sauran manyan ‘yan kwallon kafa na duniya wanda suka hada da, dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Virgil Van Dijk da Muhammad Salah da Sadio Mane da Kylian Mbappe da dai sauransu.

Wannan dai shine karo na shida da Messi ya lashe wannan kyauta, inda ya kafa tarihin zama dan wasa na farko a duniya da ya lashe wannan kyauta har sau shida.

A kakar wasanni da ta gabata Messi ya samu nasarori da dama wanda suka bashi damar lashe wannan kyauta, wanda suka hada da taimakawa kungiyarsa ta Barcelona lashe gasar La ligar kasar Spaniya, duk da dai ya kasa taimakawa Barcelona lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

A gasar La Liga Messi ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zura kwallaye karo na 6, inda yake da kwalleye 36, a yayin da ya taimaka aka zura kwallaye 13. Wanda hakan ke nuna cewa Messi na da hannu wajen zurawa Barcelona kwallaye 49 cikin kwallaye 90 da kungiyar ta zura a kakar wasanni da ta gabata.

Wannan dai shine karo na 5 da Messi yake zura kwallaye fiye da 35 a gasar La Liga. Haka kuma karo na shida yana zura kwallaye fiye da 50 a dukkanin wasanni da ya fafata a kakar wasanni guda daya.

Messi shine dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai wato Champions League, inda yake da kwallaye 12 cikin wasanni 10 da ya buga.

Haka kuma shine ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na hukumar dake shirya gasar cin kofin zakarun nahiyar turai wato UEFA.

Kwallon da Messi ya zurawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool daga bugun tazara a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai itace aka zaba a matsayin kwallo mafi kyau a kakar wasanni da ta gabata.

Jerin ‘yan wasa goma da suka fi bajinta a kakar wasannan ta 2018/2019.

  1. Lionel Messi (Barcelona and Argentina)
  2. Virgil van Dijk (Liverpool and Netherlands)
  3. Cristiano Ronaldo (Juventus and Portugal)
  4. Sadio Mane (Liverpool and Senegal)
  5. Mohamed Salah (Liverpool and Egypt)
  6. Kylian Mbappe (Paris St-Germain and France)
  7. Alisson (Liverpool and Brazil)
  8. Robert Lewandowski (Bayern Munich and Poland)
  9. Bernardo Silva (Manchester City and Portugal)
  10. Riyad Mahrez (Manchester City and Algeria)

Wannan dai shine karo na farko cikin shekaru goma babu dan wasa ko guda daya daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid cikin jerin ‘yan wasa goma da suka fi nuna bajinta a kakar wasan data gabata.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!