Labarai
CNG ta nemi kotu ta dakatar da gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar nan
A ranar Litinin ne gamayyar ƙungiyoyin Arewa wato coalition of Northern Groups CNG, suka halarci babbar kotun tarayya dake Abuja, inda ƙungiyar ta nemi a dakatar da gyaran Kundin tsarin mulkin ƙasar nan har sai an san makomar waɗanda suke iƙirarin raba Najeriya.
Shugaban gamayyar ƙungiyoyin Balarabe Rufa’i ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio, inda ya ƙara da cewa “dama dai tuni Najeriya ta saka hannu a yarjejeniya ta kasanshen afirika, kan cewa duka wata al’umma da basu gamsu da ƙasar su ba domin wani abu da ake musu na cutarwa to suna da damar ayi musu zaben raba gardama ko kuma a basu ƙasar da suka ce suna so.”
You must be logged in to post a comment Login