Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba za mu amince da raba Najeriya ba – Alhassan Rurum

Published

on

Majalisar wakilai ta ce ba za ta amince da yunkurin da wasu masu fafutukar a raba kasar nan gida biyu ke yi ba.

Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kibiya Rano da Bunkure Kabiru Alhasan Rurum ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom radio da ya gudana a safiyar yau.

“Yunkurin nasu na raba kasar nan, ba komai zai haifar ba illa raba kan kasa, domin kuwa Najeriya an samar da ita ne a matsayin tsintsiya madaurin ki daya” a cewar Rurum.

Kabiru Alhasan Rurum ya ce, matukar suka matsanta a raba kasar, babu laifi matukar za a yi ba tare da an zubar da jini ba.

Kabiru Alhasan Rurum ya Kuma ce, tsarin kundin mulkin Najeriya ya bai wa duk dan kasa dama ya zauna a inda yake so dan haka ba wata magana ta raba kasa.

“Akwai kudurori da zamu gabatar a gaban majalisa da za su kara kyautata tsarin tafiyar da harkokin kasar nan, wanda hakan ba zai samu ba har sai jihohi sun bada gudunmawar da ta kamata” inji Rurum.

Kabiru Alhassan Rurum ya kara da cewa, kamata yayi al’ummar kasar nan su mayar da hankali wajen bunkasa ta, ba maganar raba kasar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!