Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Safarar yara: Mun ceto yara 750 da aka yi fataucin su zuwa ƙasashen ƙetare – NAPTIP

Published

on

Hukumar yaƙi da fataucin bil-adama ta ƙasa NAPTIP ta ce daga watan Janairu zuwa na Oktoba na shekarar 2021 ta samu nasarar ceto ƙananan yara sama da 750 da aka yi fataucin su zuwa ƙasashen ƙetare.

Shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukumar rashen jihar Kano Aliyu Abba Kalli ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na Freedom Radiyo da yayi duba kan illar fataucin kananan yara.

Abba Kalli ya ce, mafi yawan yaran da suka ceto, binciken su ya nuna cewa an yi safarar su ne da nufin a sayar da su don ayi amfani da wasu sassan jikin su.

“A bunciken da hukumar mu ta gudanar ta gano cewar ana cire wani ɓangare na jikin ƙananan yaran da aka yi fataucin su zuwa wasu ƙasashen ƙetare, don yin kasuwancin su”.

“A shekaru takwas da suka gabata  binciken da muka yi mun gano cewa, ana fataucin yaran ne domin su yi karuwanci ko kuma aikin Otel sai dai yanzu a kan ciri wasu sassan jikin su ba tare da sanin su ba, musamman ma ƙodar su ko kuma wani muhimmin ɓangare”.

Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya sauke Bashir Lado daga shugabancin hukumar NAPTIP

Ya ci gaba da cewa “A farkon shekarar 2021 zuwa watan nan na Oktoba da ya ƙare, mun ceto yara sama da 750 wanda a kayi safarar su daga jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa da kuma Bauchi a ƙoƙarin fitar da su zuwa ƙetare”.

Kalli ya kuma ce “Sannan akwai yara sama da 80 da muka ceto wanda za’ayi safarar su daga ƙasar Libya zuwa Italiya, hakan nan ma mun gano mutanen da suke  taimakawa masu safarar ƙananan yara a jihohin Kano da Katsina.

Aliyu Abba Kalli ya ƙara da cewa a yanzu sun fara bincike dan gano wasu hukunce hukunce da za a rinƙa yiwa wanda aka kama da hannu wajen fataucin yara.

Har ma ya bada lambar kar ta kwana da za a iya samun hukumar su don kai korafi ko bayanan sirri kamar haka 07060801800.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!