Kasuwanci
Congo: Masu haƙar ma’adinai 32 sun mutu bayan karyewar Gada

Jami’ai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun ce aƙalla masu hakar ma’adinai 32 ne suka mutu bayan da wata gada ta ruguje a wata mahaƙar ma’adinan cobalt a kudu maso gabashin ƙasar.
Rahotanni sun ce an hana shiga wurin ne saboda ruwan sama mai yawa da kuma haɗarin zaftarewar ƙasa.
Masu haƙar ma’adinan sun kasance a wurin ba tare da izini ba a lokacin da lamarin ya faru.
Rahotanni daga yankin sun ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto.
You must be logged in to post a comment Login