Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masu hakar ma’adai 3 sun mutu bayan sun fada cikin cikin rami

Published

on

Yace a halin yanzu waɗan da suka jikkata suna samun kulawa a babban asibitin Anka na jahar Zamfara.

Inda Yace “Ramin haƙar ma’adanan ya ruguje ne ƴan mintuna kafin ƙarfe hudu na yammacin ranar Alhamis, ba mu san adadin mutanen da ke cikin ramin hakar ma’adinan ba, amma an gano gawarwaki uku, wasu mutum 11 kuma sun samu munanan raunuka.”

“Mutane ukun da suka rasu sun fito ne daga gundumar Yar Tsabaya ta ƙaramar hukumar Anka. Ya zuwa yanzu, ba mu da ainihin adadin mutanen da ke ciki, kuma ba za mu iya tabbatar da adadin mutanen ba saboda ramin ya kai zurfin mita 275.”

Zamfara tana da wadataccen ma’adanai da suka hada da zinare, tama, farar ƙasa, da granite da dai sauransu. Gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar sun haramta duk wani nau’i na ayyukan haƙar ma’adinan ba tare da samun umarni daga hukumomin tsaro ba.

Sai dai Mafi yawa daga cikin masu aikin haƙar ma’adanai a jihar suna aiki ne ba tare da samun lasisi ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!