ilimi
CONUA ta barranta kanta da yajin aikin ASUU

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa CONUA ta ce bata cikin yajin aikin da aka fara yau na jami’o’in Najeriya.
Shugaban ƙungiyar na kasa, Dakta Niyi Sunmonu ne ya tabbatar da haka, a wata sanarwa da ya fitar, ga manema labarai.
A cikin sanarwar Dakta Niyi ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa kungiyar ta CONUA ta shiga yajin aikin da ASUU ta fara a yau Litinin.
Ya kuma bayyana cewa, zuwa yanzu, kungiyar ba ta ayyana wani yajin aiki ba, tana kuma jajircewa wajen ganin tsarin jami’o’i ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata ta hanyar tattaunawa da gwamnati cikin lumana.
Sunmonu ya bukaci mambobin kungiyar da su ci gaba da zuwa aikin koyarwa da kuma kula da dalibai kamar yadda aka saba, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jami’o’i.
You must be logged in to post a comment Login