Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Corana : Ba a kawo mana yara rigakafi ba-ma’aikatan jinya

Published

on

A yayin da aka kwashe watanni shida da bullar cutar Covid 19 a kasar nan, wani ma’aikacin jinya da ya nemi a sakaye sunansa a nan Kano, ya ce, a watanni ukun farko da aka samu bullar wannan cutar an samu karacin masu karbar rigakafin kananan yara a asibitocin jihar Kano.

Ma’aikacin jinyar ya ce, a watanni ukun farko da cutar ta bulla, cikin watannin Maris da afrilu, da kuma Mayu, iyaye basa kai ya’yansu riga kafin, sakamakon tsoron daukar cutar Covid 19 a asibiti.

Ya kara da cewa, a watannin Yuni  da Yuli zuwa watan da ake ciki na Agusta, an samu karuwar masu zuwa karbar rigakafin.

Wakiliyarmu Shamsiyya Farouk Bello ta rawaito cewa an samu fitowar mata da yawa, sabanin farkon watannin da aka samu bular cutar ta Covid 19.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!