Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

CORONA: NYSC za ta kara sansanonin masu yiwa kasa hidima

Published

on

Hukumar lura da masu yiwa kasa hidima (NYSC), ta ce nan gaba kadan za ta kara yawan sansanonin masu yiwa kasa hidima don daukar matakan kare kai daga kamuwa da cutar  Corona da kuma harkokin tsaro.

Shugaban hukumar Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim ne ya bayyana haka a zantawar sa da manema labarai lokacin da ya kaddamar da bude sansanin ‘yan bautawa kasa rukunin A, zubi na biyu a Karu dake jihar Nassarawa.

Birgediya janar Shu’aibu Ibrahim, ya ce hukumar za ta cigaba da tuntubar hukumomin tsaro wajen bata shawarwari  kan yadda za’a tsare lafiyar masu yiwa kasa hidima daga hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Shugaban ya kara da cewa ta hanyar hakan ne kawai za a  tabbatar da kare lafiya da rayukan matasan  ba tare da jefa su cikin hatsari ba, duba da  matsalolin tsaro da wasu sassan kasar nan ke fama dashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!