Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Al’umma su rinka tsaftace muhallan su a zaman da suke na gida-Hygiene

Published

on

Shugaban makarantar koyar da aikin tsafta ta jihar Kano  Dakta Bashir Bala Getso ya ja hankalin jama’a da su rika tsaftace muhallan su tare da Samar da hanyoyin da zasu kiyaye bullar cutuka a yayin da ake zaman gida na tsawon sati guda anan Kano.

Dakta Bashir Bala Getso ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da Freedom Rediyo a wani mataki na bawa al’umma shawarwarin da zasu Kare kansu .

Ya ce, ya zama dole jama’a su kiyaye shiga cinkoso a daki guda don kiyaye kamuwa da cutar sankarau da amai da gudawa da sauran cututtuka da cunkoson jama’a ke haifarwa.

Yace dokar Hana fita don yin al’amuran yau da kullum itace hanya daya tilo da za a magance  annobar Corona a fadin Duniya.

Dakta Bashir Bala Getso ya Kuma ce ketarewa dokar na Barazana ga yaki da ita kamar yadda ya faru a sauran kasashen duniya.

Dakta Bashir Bala Getso na shawartar mutane da su rika bude tagogi da kuma rage cinkoso a daki don Kare kan su daga cututtuka masu yaduwa da saurin kisa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!