Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

COVID 19 : An bakado cibiyoyin bogi na gwajin Corona a Lagos

Published

on

Gwamnatin jihar Lagos, ta bankado tare da gargadin al’ummar jihar kan sababbin cibiyoyin bogi na gwajin cutar Corona da wasu ‘yan damfara suka bude a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar Akin Abayomi ne, ya bayyana haka a yammacin jiya Litinin ya yin tattaunawar sa da ‘yan jaridu akan sabbabbin cibiyoyin gwaji guda 10 da jihar ta bude a kananan hukumomin 10, da ake da yawaitar masu cutar.

Kwamishinan ya kara dacewa, gwamnatin jihar ba zata lamunci aikin wasu bata gari ba dake kokarin mai da hannun Agogo baya, za kuma ta soke fasfo din duk wasu matafiya da basu yarda a yi musu gwajin cutar ba.

Abayomi, yace zuwa yanzu gwamnatin jihar ta kara  yawan adadin  gwajin da ake yiwa al’umma a rana daya  daga  2,000 zuwa  3,000, domin samun saukaka lamarin da yiwuwar sawo kan cutar ko dakile ta gaba daya

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!