Connect with us

Labarai

COVID-19 An dage gasar cin kofin Nahiyar Afirka

Published

on

Hukumar shirya gasar cin kofin Nahiyar Afirka CAF ta sanar da dage gasar da za a yi a shekarar 2021 zuwa watan Janairun 2022.

Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan annobar Covid-19 da ake fama da ita da ta addabi duniya.

Tun farko an tsara gudanar da gasar cin kofin Afirka a watan Janairun shekarar 2021.

Haka zalika hukumar CAF ta sanar da cewa an dage gasar cin kofin nahiyar Afirka na kungiyoyin da ke taka leda a cikin gida wato CHAN da aka tsara za a yi a watan Afrilu, yanzu haka dai an shirya gudanar da gasar a watan Janairun 2021.

Kasar Kamaru ce dai zata karbi bakuncin wasannin da za a yi na gasar cin kofin Afirkan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 330,185 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!