Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Covid-19: Babu hada sahun Sallah a Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce daga ranar Jumu’a ta dakatar da jama’a daga hada sahun sallah domin kaucewa cakuduwa a tsakanin jama’a.

Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a birnin Dutsen jihar Jigawa.

Wakilin mu Aminu Umar Shuwajo ya rawaito mana cewa gwamnan ya ce daga yanzu gwamnatin jihar Jigawa ta dakatar da duk wani taron daurin aure, ko suna da duk wani taron jama’a a jihar.

Wannan mataki da gwamnatin jihar Jigawa ta dauka na zuwa ne kasa da awanni da dokar hana fita da zaman kulle wadda makociyar ta wato jihar Kano ta sanya kuma za ta fara aiki a daren Alhamis.

Har izuwa yanzu dai ba a samu bullar cutar ta Corona a jihar Jigawan ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!