Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid -19:Attajirai su tallafawa masu karamin karfi-Shehu Ashaka

Published

on

Wani babban dan kasuwa  Alhaji Shehu Ashaka,  ya ja hankalin mawadata a  fadin jiha wajen bada gudunmowa da za ta ragewa mutane  radadin kuncin  rayuwa da ake ciki  musamman bayan bullar  cutar Corona a kasar nan.

Alhaji Shehu Ashaka ya bayyana hakan ne yayin da yake bada tallafin kayan masarufi na shinkafa buhu 400 da katan- katan na taliya da sauran kayan masarufi.

Labarai masu alaka.

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta bada umarnin bayar da tallafi ga mabukata

Covid-19: Maryam Abacha ta tallafawa mabukata da kayan abinci

A nashi jawabin  shugaban cigaban  karamar hukumar Tsanyawa Alhaji Sanusi Abdullahi Nassarawa, ya ce baza suyi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun tallafawa mutanen da suka fito daga yankin Tsanyawa.

Umar Idris Shu’aibu wakilin mu da ya halarci taron rabon  ya ruwaito cewar dattawan yankin sun yi alakawarin raba kayan tallafin ga garuruwan Dagatai da suke da su 21, bisa adalci da cancanta don saukaka wa talakawa yanayin halin  da ake ciki a yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!