Labarai
Covid-19: Gwamnatin tarayya ta fitar da tan dubu 70 na abinci don tallafawa mabukata-Nanono
Gwamnatin tarraya ta bayyana cewa a yanzu haka an fitar ta tan dubu 70 na kayan abinci da suka hadar da Gero Masara da Dawa da kuma garin Rogo domin tallafawa al’umma don takaita wa mutane halin kunci da suke ciki a game da annobar cuar Covid-19.
Ministan ayyukan gona da raya karkara, Alhaji Sabo Nanono ne ya bayyana hakan jim kadan bayan shirin barka da hantsi na nan tashar freedom radiyo wanda ya mai da hankali kan tattaunawa kan rabon kayyayakin abincin.
Alhaji Sabo Nanono ya kuma kara da cewar jihohin da za’a rabawa kayan masarufin sun hadar da Lagos da Abuja da Ogun wanda gwmnatin tarraya ta bada umarnin hana zirga-zirga a cikin su, baki daya sai kuma jihohin Zamfara da Barno da kuma Adamawa wanda su ke fama da ayyukan ‘yan ta’adda.
Ministan Noma ya kuma ce matsalar matsin talauci da kasar nan ke fuskanta na da nasaba da yadda aka mayar da hankali kan dogara da man fetur, aka kuma yi watsi da bangaren noma.
Alhaji Sabo Nanono ya kuma bayyana cewa tuni ma’aikatar aikin gona ta fara shirye-shirye domin tunkarar damunar bana da kuma daukan matakan da suka kamata don ganin an tafiyar da noman bana yadda ya dace.
You must be logged in to post a comment Login