Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Covid-19: Yan kasuwar sabon gari su rinka tsaftace kasuwar-Nuhu Indabo

Published

on

Sarkin kasuwar Sabon gari Alhaji Nafiu Nuhu Indabo, ya yi kira ga mutanen dake gudanar da kasuwanci a kasuwar da su dage wajen kula da tsaftar guraren da suke gudanar da kasuwanci dake ciki da wajen kasuwar.

Nafi’u Nuhu Indabo ya bayyana hakan ne yayin da suke gudanar da Feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka a masallatan da ke cikin kasuwar.

Alhaji Nafi’u Nuhu Indabo ya kuma ce Duba da irin hatsarin da cutar Covid-19 take dashi ne ya sanya suka gudanar da feshin dan kare lafiyar al’ummar dake shiga kasuwar dama ‘yan kasuwar.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwar ta Abubakar Rimi sun bayyan farin cikin su bisa aikin feshin da akai musu.

Sun kuma yi kira ga gwamnati da hukumar NCDC da su dinga gudanar da feshi a cikin kasuwar Duba da yawan mutanan da take diba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!