Labarai
Covid 19: Maniyyatan Indonesia ba zasu Hajji ba
Kasar Indonesia, ta sanar dacewar al’ummar kasar ba zasu yi aikin Hajjin bana ba.
Ministan harkokin addinai na kasar ta Indonesia, Fachrul Razi, ya bayyana haka a yau ga manema labarai a birnin Jakartaa.
Fachrul Razi, yace gwamnatin kasar ta Indonesia, ta yanke shawarar daukar matakin ne kasancewar mahukuntan kasar Saudi Arabia, basu bada tabbacin gudanar da aikin Hajjin bana ba.
Labarai masu alaka.
Hukumomi a kasar Saudia zasu dawowa da maniyyata kudaden su
Kasar Saudiya ta dakatar da zuwa Umara
Ministan ya kara dacewa, hakan kuma yana daga cikin matakan kariya na lafiyar al’ummar kasar, wanda matsayar ta biyo bayan tattaunawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a harkokin lafiya da aikin Hajji na kasar.
Kasar ta Indonesia, ta kasance kasar da tafi kowa yawan alhazai da suke zuwa aikin Hajji, da take da yawan alhazai dubu dari biyu da ashirin da daya, da mahukuntan kasar Saudia ta warewa mahajjatan kasar a bana.
You must be logged in to post a comment Login