Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Covid 19: Maniyyatan Indonesia ba zasu Hajji ba

Published

on

Kasar Indonesia, ta sanar dacewar al’ummar kasar ba zasu yi aikin Hajjin bana ba.

Ministan harkokin addinai na kasar ta Indonesia, Fachrul Razi, ya bayyana haka  a yau ga manema labarai a birnin Jakartaa.

Fachrul Razi, yace gwamnatin kasar ta Indonesia, ta yanke shawarar daukar matakin ne kasancewar mahukuntan kasar Saudi Arabia, basu bada tabbacin gudanar da aikin  Hajjin bana ba.

Labarai masu alaka.

Hukumomi a kasar Saudia zasu dawowa da maniyyata kudaden su

Kasar Saudiya ta dakatar da zuwa Umara

Ministan ya kara dacewa, hakan kuma yana daga cikin matakan kariya na lafiyar al’ummar kasar, wanda matsayar ta biyo bayan tattaunawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a harkokin lafiya da aikin Hajji na kasar.

Kasar ta Indonesia, ta kasance kasar da tafi kowa yawan alhazai da suke zuwa aikin Hajji, da take da yawan alhazai dubu dari biyu da ashirin  da daya, da mahukuntan kasar Saudia ta warewa mahajjatan kasar a bana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!