Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Covid-19: Masana a Kano sun yi tsokaci kan Coronavirus

Published

on

Wani Malami a sashen koyar da ilimin addinin musulunci a jami’ar Bayero dake nan Kano, Dakta Aminu Isma’il Sagagi ya bayyana cutar COVID-19 wato Coronavirus a matsayin babbar annobar da Allah kan jarabci al’umma da ita, wadda ta shafe sauran nau’o’in cutukan da ake fama da su saboda illar da cutar ta ke dashi ga lafiyar al’umma.

Malamin ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Duniyar Mu A Yau na nan gidan Freedom Rediyo da ya maida hankali kan mahangar addinin musulunci kan annobar cutar ta COVID-19 da take barazana ga lafiyar al’umma a wasu kasashe a fadin duniya.

Dakta Abdulkadir Isma’il, da Farfesa Ahmad Murtala sai kuma Dakta Aminu Isma’il Sagagi.

Haka kuma, Dakta Mu’azzam Sulaiman, ya ce addinin musulunci ya umarci musulmai da cewa idan Allah ya jarabceku da wata annoba ko masifa a wani yanki na kasar ku ko kuma a wata kasar daban, to ya zama wajibi ga ma zauna yankin kada su fita daga ciki, haka suma wadan da basa cikin yankin kada su shiga, don samun damar takaita yaduwar annobar.

Karin labarai:

Covid19: Gwamnatin Kano ta samar da lambobin kira kan Coronavirus

Covid19: Babu dan kasar nan daya kamu da cutar Corona Virus.

A nasa bangaran, Farfesa Ahmad Murtala da ya kasance a cikin shirin ce wa ya yi hakika addinin Musulunci ya koyar da cewa duk wani gari da aka tsinci kai cikin halin annoba to wajibi ne a killace kan iyakokin sa ba shiga ba fita kamar yadda ya faru a zamanin sayyadina Umar.

Shima Dakta Abdulkadir Isma’il daya daga cikin bakin, ya ce yawaitar yaduwar annoba ko cuta a duniya wata alama ce da ke nuna yadda al’umma suke yin shakulacin bangaro da tsallake dokokin ubangiji da kuma sakaci da yin ibada kamar yadda addini musulunci ya tanada.

Dukkannin bakin sunyi kira ga al’ummar musulmai da su ci gaba da yin addu’o’I ga ubangiji tare da bin dokokin kariya daga kamuwa da cutar don takaita yaduwar cutar a kasar baki daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!