Coronavirus
COVID-19: yadda al’ummar Kano suke gudanar da zaman gida
A lokacin da al’ummar jihar Kano suka shiga kwanaki na biyu na dokar hana fita da gwamnatin jihar Kano ta saka sun ci gaba da bayyana yadda zaman gidan ya saka su cikin wani hali.
A wasu manyan tituna na cikin birnin Kano wasu daga cikin al’ummar Kano sun ci gaba da fitowar da ta zame musu dole.
Wakilinmu Abbas Yushau Yusuf yayi kicibis da wasu daga cikin mutanan jihar Kano na tafiyar kasa a bakin titi ya tattauna da su dalilan da yasa suka fito inda suka bayyana masa cewa zaman gidan ne suka gaji dashi.
Shima wani daga cikin su Ahmad Isa da tafiyar kasa ta kama shi kuma ta dole yace ya bar unguwar su ne mai nisan gaske domin karbowa mahaifiyar sa magani.
Mun tuntubi shugaban kwamitin tattara taimako na yaki da cutar Corona ta jihar Kano kuma shugaban jamiar Bayero Farfesa Muhammad Yahuza Bello yace har yanzu Kwamitin na shirye shiryen yadda zasu fara raba tallafin.
Farfesa Muhammad Yahuza Bello yace tunda baa samu karin wasu kudade masu yawa daga miliyan dari uku da sabain da shida da aka tara tunda fari ba har yanzu shirin nasu na mutum dubu hamsin ne kamar yadda aka tsara.
You must be logged in to post a comment Login