Connect with us

Labarai

Covid 19- ‘Yan Najeriya uku sun mutu a Amurka

Published

on

Karamin jakadan kasar nan a birnin New York, na kasar Amurka, Benaoyagha Okoyen, ya sanar da  cewar  zuwa yanzu haka ‘yan Najeriya uku ne suka rasu a kasar Amurka, sakamakon kamuwa da  cutar Corona.

Jakada Okoyen, ya bayyan hakane ga kamfanin dillacin labaran kasar a wata takarda da ya aike musu dangane da halin da mazauna kasar ta Amurka ‘yan asalin  kasar nan ke ciki.

Ya kara da cewa akwai likita dan jihar Abia da ya kamu sakamakon aikin dakile cutar a birnin na New York,   sai dalibi  Bassey Offiong, mai shekaru 25, dake  karatu a jami’ar  Western Michigan, sai Hajiya Laila Abubakar Ali, mai shekaru 60, yar asalin jihar Kano, da ta mutu a ranar 25 ga watan Maris.

Labarai masu alaka.

Covid-19: Abokan mataimakin shugaban kasa za su bayar da tallafin naira Miliyan 100

Covid-19: Buhari zai rabawa al’ummar Kano sama da naira biliyan daya

Sanarwar ta kara dacewa na ukun Dakta, Caleb Anya,dan asalin jihar  Abia ya rasu ne ranar daya ga watan Afrilu a birnin na  New York, a kokarin da yake na ceto wasu daga cutar ta Coruna Virus.

Jakada, Okoyen , ya mika sakon alhini da ta’aziyya ga ‘yan uwan mamatan  a wannan hali na alhini da annoba da ake  cikin ta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!