Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Covid-19: Abokan mataimakin shugaban kasa za su bayar da tallafin naira Miliyan 100

Published

on

Abokan mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, za su bai wa wasu kananan yan kasuwa a kasar nan guda dari, wadanda suka gabatar tsarin gudanar da kasuwancin su wato ‘Business Proposals’ tallafin naira miliyan daya-daya don bunkasa harkokinsu.

A cewar abokan mataimakin shugaban kasar, wannan wani tallafi ne da suke son bayarwa a matsayin wani bangare na ci gaba da bikin cika shekaru sittin da uku da haihuwar farfesa Yemi Osinbajo.

Wadanda suka shirya taron dai sun ce, wadanda za su ci gajiyar tallafin wadanda aka zaba ne a yayin wani taro da aka shirya ga masu kananan sana’oi a ranar takwas ga watan jiya na Maris.

A ranar takwas ga watan jiya na Maris din ne dai, mataimakin shugaban kasa farfesa Yemo osinbajo, ya cika shekaru sittin da takwas a duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!