Connect with us

Labaran Wasanni

COVID-19: ‘Yan wasa da jami’ai 36 sun kamu

Published

on

Kimanin ‘yan wasa da jami’ai talatin da shida ne a cikin kungiyoyi ashirin dake buga wasa a gasar firimiyar kasar Ingila suka kamu da cutar Korona a wannan watan na Janairu.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata nasarawa da hukumar gudanar da gasar ta wallafa a shafinta na Internet.

Hukumar ta ce an samu mutane ashirin da bakwai da aka yiwa gwaji daga ranar hudu zuwa takwas ga watan Janairun bayan haka aka samu Karin mutane goma tsakanin ranar Juma’a zuwa Lahadi da suka gabata.

An dai gudanar da gwaji har zagaye biyu kan ‘yan wasan da kuma jami’an kimanin dubu biyu da dari biyar da casa’in da uku, yayin da sakamakon ya nuna mutane talatin da shida na dauke da cutar.

Sanarwar ta kuma ce, duk wanda ya kamu da cutar ta Korona zai killace kansa tsawon kwanaki goma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!