Connect with us

Coronavirus

Covid-19: Za a rufe karin garuruwa 3 a Jigawa

Published

on

Gwamnatin Jihar jigawa ta sanya dokar zaman gida na tsawon mako guda daga 12 daren ranar alhamis a karamar hukumar Birnin Kudu da garin Gumel da kuma Gujungu ta karamar hukumar Taura.

Gwamnatin Jigawa ta sanya wannan doka ne sakamakon samun karin mutane biyu da aka samu dauke da cutar COVID-19.

Gwamnan jihar jigawa Alh. Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka da yammacin ranar talata.

Gwamnan ya kara da cewa an samu masu dauke da cutar ne sun zo daga wasu wurare mabam-bamta.

Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito gwamnan na cewa, gwajin da aka dauka na mutane 17 da sukayi mu’amala da wanda aka samu yana dauke da cutar 16 daga ciki sakamakonsu ya fito basa dauke da cutar saura mutum guda da ake dakonsa, wanda da zarar gwajin ya fito babu cutar za saki garin Kazaure.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,762 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!