Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

COVID-19 : Za’a kara yiwa ‘yan wasan Super Eagles gwaji a karo na 2 – NFF

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta ce za a kara yi wa daukacin tawagar ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles gwajin cutar Corona karo na biyu, ya yin da suke tunkarar wasan sada zumunta da za su fafata da kasar Tunisia a gobe Talata.

An dai yiwa daukacin tawagar ‘yan wasan gwajin cutar a makon da ya gabata amma babu wanda ya kamu da cutar kafin wasan su da Algeria na ranar Juma’ar makon jiya da aka yiwa Najeriya ci daya mai ban haushi.

Ba dan wasan Najeriya cikin ‘yan wasa masu daraja a Afrika

Akwai bukatar sabbin masu horaswa 11 da aka nada su ciyar da kungiyoyin wasannin Najeriya gaba – Moukhtar

Dan wasan Liverpool Thiago Alcantara ya kamu da Corona

NFF ta kuma ce, tawagar ‘yan wasan sun dawo hayyacin su daga cin da Algeria ta yi musu, ya yin da ake tsammanin zasu gudanar da wasa mai kyau idan suka hadu da Tunisia a goben.

Mun gudanar da atisaye sosai bayan fafatawar mu da Algeria kuma muna fatan samun nasara kan Tunisia a ranar Talata” kamar yadda jami’in yada labaran kungiyar Toyin Ibitoye ya ce.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!