Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ba dan wasan Najeriya cikin ‘yan wasa masu daraja a Afrika

Published

on

Wasu daga cikin al’ummar Najeriya sun koka bisa rashin samun koda dan wasa daya na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles cikin jerin ‘yan wasan da suke da daraja a Afrika.

A satin nan da muke ciki ne dai aka fitar da jerin sunayan ‘yan wasa 10 daga Afrika dake da daraja a fagen kwallon kafa.

Daga cikin jerin sunayan ‘yan wasan a kwa ‘yan wasa biyu daga kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar Ingila Mohammed Salah dan kasar Masar da kuma Sadio Mane, daga kasar Senegal.

‘yan wasan biyu sadio Mane da Muhammad Salah darajarsu dai ta kai yiro miliyon 120.

Dan wasan Najeriya ya kamu da Corona

Manchester na neman tsawaita kwantaragi da Pogba

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles da darajarsa tai kusa da shiga jerin sunayan ‘yan wasan dake da darajar a Afrka shine dan wasan kungiyar Leicester City ta kasar Ingila, Wilfred Ndidi, wanda darajarsa takai Yiro miliyon 36.

Cikin sunayan ‘yan wasa 10 a kwai ‘yan wasa biyu-biyu daga kasar Senegal da kasar Ivory Coast da kuma kasar Morocco.

Sai kuma ‘yan wasa dai-dai daga kasar Masar da Gabon da Algeria da kuma kasar Ghana.

Magoya bayan kungiyar ta Super Eagles dai a Najeriya sun bayyana mamakin su bisa rashin samun sunan dan wasan Najeriya dake wasa a kungiyar Lille ta kasar Faransa Victor Osimhen daga cikin jerin ‘yan wasan 10 dake da daraja a yankin na Afrika.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!