Connect with us

Labaran Wasanni

Cristiano Ronaldo ya kamu da Coronavirus

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta kasar Portugal ta tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar Corona.

Hukumar ta bayyana haka ne a shafin ta na Internet a yau Talata, inda ta ce ba zai buga wasan da kasar zata yi da Sweden a gobe Laraba ba.

Ronaldo mai shekara 35 wanda ya samu lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar, ya buga wa kasar sa ta Portugal wasan ta da Faransa a ranar Lahadin data gabata.

Hukumar ta kuma ce, “Bayan gwajin ‘yan wasan da aka yi a safiyar yau Talata, an samu Ronaldo dauke da cutar amma dukkanin sauran ‘yan wasan na cikin koshin lafiya”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!