Connect with us

Labaran Wasanni

Cavani ba zai buga wa Man United wasan ta na farko ba

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ce Edinson Cavani ba zai samu shiga cikin ‘yan wasan da zasu fafata da Newcastle United a ranar Asabar mai zuwa ba.

United ta tabbatar da haka ne bayan Cavani ya sauka a Ingila daga Faransa lamarin da ya sanya dole ya killace kansa tsawon makonni biyu don kaurace wa cutar Corona.

Cavani ya koma United a matsayin kyauta a ranar karshe ta hada-hadar ‘yan wasa ta bana, sai dai ya zama wajibi ga duk wani bako da ya shiga Ingila ya kiyaye doka da ka’idojin kamuwa da COVID-19 a kasar.

Manchester United za ta kece raini da Newcastle United a ranar Asabar 17 ga wannan watan da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!